Yanzu masu amfani da wayoyin android suna iya kallon tashoshin TV a wayar su ba tare da amfani da 'Adobe flash player' ba.
Ana yin hakan ne ta hanyar amfani da wani 'Application' mai suna 'Sybla TV' wanda ke kunshe da tashoshin kasashen larabawa (Arabian channels) da dama. Kaman masu nuna wasanni (sports) da na fina-finai da na labarai iri-iri. Wato irin su MBC, MBC 2, MBC 4, National Geographic, Aljazeera sports, Skysports, MBC Action, Nessma tv, da dai sauran su.
Duk mai bukatan saukar da wannan application na 'sybla tv' a wayar sa ta Android, sai ya [Latsa nan] ko kuma kai tsaye a ziyarci http://sybla.com
Abin ban sha'awa ne da ƙayatarwa mutum ya ga ya kamo tashoshin kasashen waje a kan wayar sa, a duk inda ya ga dama, kuma na tabbata wannan zai taimaka musamman a lokacin da mutum bai son wani shiri na TV ya wuce shi.
Kar ka/ki manta! :) Gayyato yan'uwa da abokai na dandalin facebook da twitter zuwa wannan shafin.
No comments:
Post a Comment